An gano dumbin dalolin jabu a wani kango a Arewacin Najeriya

An gano dumbin dalolin jabu a wani kango a Arewacin Najeriya

- An gano dumbin kudaden jabu a wani kango a Arewacin Najeriya

- An ga kudaden ne a garin Maiduguri

- Kudaden suna da yawa kuma daloli ne

Jami'an tsaron farar hula a Najeriya shiyyar jihar Borno, a garin Maiduguri sun sanar da samun nasarar gano wasu makudan kudaden kasar Amurka na jabu da suka kai darajar dala 144,000 a wani kangon gida dake a rukukin gidaje masu saukin kudi na Sahagari a garin na Maiduguri.

An gano dumbin dalolin jabu a wani kango a Arewacin Najeriya

An gano dumbin dalolin jabu a wani kango a Arewacin Najeriya
Source: Instagram

KU KARANTA: SDP tayiwa Ambode tayin tikitin kujerar gwamna

Kwamandan rundunar, Ibrahim Abdullahi shine ya sanarwa da manema labarai hakan lokacin da yake zantawa da su a ranar Juma'a a garin na Maiduguri.

Legit.ng ta samu cewa wani magidanci ne mai suna Bukar Goni ya zo ya fadawa jami'an haka inda su kuma suka je suka bincika suka kuma yi nasarar dauko su.

A wani labarin kuma, Jami'an tsaro a Najeriya sun sanar da samun nasarar chafke wasu masu bada kwarmato su biyu watau Mista Prince Jeff Ove, dan shekara 37, daga jihar Bayelsa, da kuma Mohammed Sanusi, dan shekara 39, daga jihar Kogi kan bayar da kwarmaton karya.

Majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai ta ruwaito cewa su dai masu bayar da kwarmaton sun sun kai kwarmaton karya ne a game da Mista Emmanuel Mbaka daya daga cikin shugabannin bankin tallafin gidaje na kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel