Kwamitin Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati

Kwamitin Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati

- Kwamitin Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun jami'an gwamnati

- Jami'an tsaffin ma'aikatan gwamnati ne

- A kwanan baya ne SHugaba Buhari ya kafa kwamitin

Kwamiti na musamman da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada domin kwato dukkan dukiyar al'ummar da wasu ma'aikatan gwamnati suka yi sama da fadi da su a cikin garin Abuja ya samu nasarar kwato motoci 19.

Kwamitin Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati

Kwamitin Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Za'a bude sabuwar matatar mai a Najeriya

Motocin dai kamar yadda muka samu, kwamitin ya kwato su ne daga hannun tsaffin ma'aikatan hukumar nan ta kidayar al'umma ta kasa watau National Population Commission (NPopC)a turance.

Legit.ng haka zalika ta samu cewa su dai motocin tun farko an zargin tsaffin kwamishinonin hukumar ne da tafiya da su bayan da suka kammala wa'adin mulkin su duk da rashin kyautawar hakan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a farkon hawa bisa karagar mulki, shugaba Muhammadu Buhari a kokarin sa na ganin ya killace dukiyar al'umma daga barayi, ya kafa kwamitin da zai taimaka masa wajen kwato kadarorin gwamnati dake hannun wasu.

A wani labarin kuma, Dakta Adetokumbo Pearse, dake zaman shugaban tsare-tsare da tattara jama'a na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a ranar Juma'a ya bayyana cewa a shirye suke da su baiwa gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode tikitin takara a jam'iyyar su.

Mista Adetokumbo ya bayyana cewa su a matsayin su na jam'iyyar adawa, a shirye suke su ba gwamnan tikiti a wurin su idan har jam'iyyar sa ta APC ta hana shi a zaben fitar da gwanin da za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel