Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga rundunar sojin sama bisa rasuwar Baba Ari

Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga rundunar sojin sama bisa rasuwar Baba Ari

- Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya da jajae ga NAF bisa rasuwar jami'inta sakamakon hatsarin jiragen yakin sama

- Shugaban kasar ya zayyana kyawawan ayyukan mamacin yana mai cewa gudunmowarsa ga Nigeria ba zaya taba tafiya a banza ba

- Buhari ya yi addu'ar samun saukin sauran jami'an biyu, yana mai tabbatar masu cewar addu'ar 'yan Nigeria na tare da su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya tare da jajantawa ga rundunar sojin sama ta kasa NAF a ranar Juma'a, bisa rasuwar daya daga cikin matukan jiragen yakin sojin saman a wani hatsari da jiragen biyu suka yi a Abuja.

Shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyya na musamman ga shugaban tawagar matukan jirgin MB Baba-Ari, jami'in sojin da ya gamu da ajalisansa sakamakon hatsarin, yayinda ya ke kuma jajantawa sauran jami'an sojin biyu da ke kwance asibiti da fatan samun lafiyarsu cikin gaggawa.

A cikin jawabin jawabin ta'aziyyar da jajantawa, wanda shugaban rundunar sojin sama ta kasa, Air Marshal Abubakar Siddique ya karanta a wajen bizne gawar Baba-Ari a Abuja, shugaban kasar ya zayyana kyawawan ayyukan mamacin yana mai cewa gudunmowarsa ga Nigeria ba zaya taba tafiya a banza ba.

KARANTA WANNAN: Hotunan jana'izar jami'in sojan da ya rasu a hadarin jirgin

Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga rundunar sojin sama bisa rasuwar Baba Ari

Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga rundunar sojin sama bisa rasuwar Baba Ari
Source: Facebook

Ya bada tabbacin cewa, sojin ya sadaukar da rayuwarsa a lokacin da kasar ke bukatarsa don bukin taya Nigeria murnar cika shekaru 58 da samun 'yancin kai. Ya kuma yi addu'ar Allah ya sa Aljannah ta zamo makomar karshe ga mamacin, kana Ya baiwa iyalai da yan uwan mamacin hakurin jure wannan babban rashi.

Wakilan shugaban kasar sun kuma ziyarci sauran jami'an sojin biyu, SL Abatuba da kuma Laftanar Ambi da suke kwance a asibiti tare da shaida masu sakon shugaban kasar a garesu. Buhari ya yi addu'ar samun saukinsu, yana mai tabbatar masu cewar addu'ar 'yan Nigeria na tare da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel