Buhari ya samu karramawa na musamman a Amurka

Buhari ya samu karramawa na musamman a Amurka

A ranar Juma’a, 28 ga watan Satumba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari karramawa biyu yayinda jihar New Jersy da birnin Philadelphia suka yi mah yabo na musamman.

Buhari ya yi wani jawabi akan cin hanci da rashawa, hijira da kuma dinke barakar ayyukan ci gaba a Afrika, shirin da aka yi a taron majalisar dokokn kasar karo na 73.

Bayan jawabin, Diane Campbell, dake wakiltan Sanata Turner na New Jersy, ya fito gaba ya karanta wani jawabi na Buhari, inda a yaba ma dakarun sojinsa, kwarewasarsa dakuma manufofin siyasarsa.

Buhari ya samu karramawa na musamman a Amurka

Buhari ya samu karramawa na musamman a Amurka

Shugaban Najeriyan wanda ya kasance cikin mamaki kuma karramawar uayazo masa a bazata ya tashi tsaye ya kame yayinda akn taron ya kaure da tafi.

Shugaban kungiyar kasuwanci da zuba jaria Najeriya, Dr Jude Iheoma yak ma karanta wani jawabin Buhari a mdain birnin Philadelphia.

Buhari ya samu karramawa na musamman a Amurka

Buhari ya samu karramawa na musamman a Amurka

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ýar majalisar wakilai Funke Adedoyin ta mutu

Wadanda suka shaidi wannan karramawar sun hada da shugabannin kamfanonin masu zuba jari na kasa da kasa, ministoci, darakta-Janar da Dr Ibrahim Mayaki, shugaban kungiyar ci gaban Afrika (NEPAD).

Misis Gloria Akobundu, shugabar NEPAD Najeria; Farfea Ibrahim Gambari, tshon ministan harkokin waje, da manyan jami’an wamnatin Najeriya ma sun halarci taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel