Shugaba Buhari yayi wa manyan kasar nan wankin babban bargo

Shugaba Buhari yayi wa manyan kasar nan wankin babban bargo

- Shugaba Buhari yayi wa manyan kasar nan wankin babban bargo

- Yace a baya sun yi shiru sadda ake ta lalata kasa

- Yace amma yanzu sai ga shi sun fito suna ta surutu

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda yace wadanda ke kiran kan su manya a Najeriya suka yi shiru shekaru 16 lokacin da jam'iyyar PDP ke mulkin kasa duk kuwa da yadda suka lalata kasar.

Shugaba Buhari yayi wa manyan kasar nan wankin babban bargo

Shugaba Buhari yayi wa manyan kasar nan wankin babban bargo
Source: Facebook

KU KARANTA: Za'a bude sabuwar matatar mai a Najeriya

Ya kara da cewa hakan haka zalika abun takaici ne yadda kuma yanzu wasun su ke ta kumfan baki suna cewa wai baya da sauri bayan duka-duka shekaru 3 kadai yayi yana mulki.

Legit.ng ta samu cewa mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin New York, kasar Amurka.

Mista Adesina ya ce shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wasu 'yan asalin Najeriya dake zaune a kasar ta Amurka.

A wani labarin kuma, Dakta Adetokumbo Pearse, dake zaman shugaban tsare-tsare da tattara jama'a na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a ranar Juma'a ya bayyana cewa a shirye suke da su baiwa gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode tikitin takara a jam'iyyar su.

Mista Adetokumbo ya bayyana cewa su a matsayin su na jam'iyyar adawa, a shirye suke su ba gwamnan tikiti a wurin su idan har jam'iyyar sa ta APC ta hana shi a zaben fitar da gwanin da za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel