Jam'iyyar SDP tayi wa gwamnan jihar Legas, Ambode tayin tikitin takara

Jam'iyyar SDP tayi wa gwamnan jihar Legas, Ambode tayin tikitin takara

- Jam'iyyar SDP tayi wa gwamnan jihar Legas, Ambode tayin tikitin takara

- Ana tunanin dai da wuya ya samu tikitin takara a APC

- Ana zargin Ambode da Tinubu din sun yi fada ne

Dakta Adetokumbo Pearse, dake zaman shugaban tsare-tsare da tattara jama'a na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a ranar Juma'a ya bayyana cewa a shirye suke da su baiwa gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode tikitin takara a jam'iyyar su.

Jam'iyyar SDP tayi wa gwamnan jihar Legas, Ambode tayin tikitin takara

Jam'iyyar SDP tayi wa gwamnan jihar Legas, Ambode tayin tikitin takara
Source: Facebook

KU KARANTA: Wani tsohon gwamna a Arewa ya shiga takarar dan majalisar wakilai

Mista Adetokumbo ya bayyana cewa su a matsayin su na jam'iyyar adawa, a shirye suke su ba gwamnan tikiti a wurin su idan har jam'iyyar sa ta APC ta hana shi a zaben fitar da gwanin da za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.

Legit.ng ta samu cewa shi dai gwamnan na Legas na fuskantar barazanar rasa tikitin takara a APC bayan dan sabanin da ake tunanin sun samu da tsohon gwamnan jihar kuma jigo a jam'iyyar APC, Cif Bola Tinubu.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda yace wadanda ke kiran kan su manya a Najeriya suka yi shiru shekaru 16 lokacin da jam'iyyar PDP ke mulkin kasa duk kuwa da yadda suka lalata kasar.

Ya kara da cewa hakan haka zalika abun takaici ne yadda kuma yanzu wasun su ke ta kumfan baki suna cewa wai baya da sauri bayan duka-duka shekaru 3 kadai yayi yana mulki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel