An cafke masu bada kwarmato 2 da suka shirga karya kan wani manajan banki a Najeriya

An cafke masu bada kwarmato 2 da suka shirga karya kan wani manajan banki a Najeriya

- An cafke masu bada kwarmato 2 da suka shirga karya kan wani manajan banki a Najeriya

- Matasan 2 sun bayar da kwarmaton karya

- Yin hakan ya sabawa dokar kasa

Jami'an tsaro a Najeriya sun sanar da samun nasarar chafke wasu masu bada kwarmato su biyu watau Mista Prince Jeff Ove, dan shekara 37, daga jihar Bayelsa, da kuma Mohammed Sanusi, dan shekara 39, daga jihar Kogi kan bayar da kwarmaton karya.

An cafke masu bada kwarmato 2 da suka shirga karya kan wani manajan banki a Najeriya

An cafke masu bada kwarmato 2 da suka shirga karya kan wani manajan banki a Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta soma bibiyar kashe kudaden yan siyasa

Majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai ta ruwaito cewa su dai masu bayar da kwarmaton sun sun kai kwarmaton karya ne a game da Mista Emmanuel Mbaka daya daga cikin shugabannin bankin tallafin gidaje na kasa.

Legit.ng ta samu cewa mai magana da yawun kwamiti na musamman da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kafa domin kwato dukiyar kasa daga hannu tsaffin jami'an gwamnati, Lucie-Ann Laha ce ta shaidawa manema labarai hakan a garin Abuja.

A wani labarin kuma, Jami'an tsaron farar hula a Najeriya shiyyar jihar Borno, a garin Maiduguri sun sanar da samun nasarar gano wasu makudan kudaden kasar Amurka na jabu da suka kai darajar dala 144,000 a wani kangon gida dake a rukukin gidaje masu saukin kudi na Sahagari a garin na Maiduguri.

Kwamandan rundunar, Ibrahim Abdullahi shine ya sanarwa da manema labarai hakan lokacin da yake zantawa da su a ranar Juma'a a garin na Maiduguri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel