APC ta hana ministocin Buhari 2 takarar gwamna

APC ta hana ministocin Buhari 2 takarar gwamna

Jam'iyyar All Progressives Congress ta fitar da jerin sunayen yan takarar da ta tantance neman kujeran gwamna a jihohin kasar.

Abun mamaki sai gashi ba ta tantace wasu minsitocin Shugaban kasa Muhammadu Buhari guda biyu da ke son tsayawa takarar ba.

Ministocin dai sun hada da Barista Adebayo Shittu na ma'aikatar sadarwa wanda ke takarar gwamnan jihar Oyo da kuma Aisha Jummai Alhassan ministar harkokinmata, dake takarar gwamnan jihar Taraba.

Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce ba ta tantance Barista Adebayo ba ne daga cikin 'yan takarar gwamna takwas na jihar, saboda rashin shaidar yi wa kasa hidima da ba shi da ita.

APC ta hana ministocin Buhari 2 takarar gwamna

APC ta hana ministocin Buhari 2 takarar gwamna
Source: UGC

Tuni dai Mista Shittu ya sauka daga kujerarsa don tsayawa takarar gwamnan.

Amma sanarwa ba ta bayyana dalilin da ya sa ba a tantance Aisha Jummai Alhassan a matsayin 'yar takarar gwamnan Taraba ba daga cikin mutum 12 da suke takarar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ýar majalisar wakilai Funke Adedoyin ta mutu

Sai dai za a iya tuna cewa Aisha Alhassan ta nuna biyayyarta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda ake ganin ubangidanta ne a siyasance, kan goyon bayansa a takarar shugabancin kasar nan, tun ma kafin ya koma babbar jam’iyyar adawar kasar wato PDP.

Wannan dalili ne ya sa ake ganin jam'iyyar APC na iya kin tantance ministar, ko da yake dai jam'iyyar ba ta yi wani karin bayani kan dalilin rashin tantance ta din ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel