Shehu Sani: Hanyoyi 6 na kawo karshen saye da sayar da kuri'u a wajen zabe

Shehu Sani: Hanyoyi 6 na kawo karshen saye da sayar da kuri'u a wajen zabe

- Sanata Shehu Sani, ya bayyana hanyoyi 6 na kawo karshen saye da sayar da kuri'u a yayin gudanar da zabe a kasar

- Wannan shawarar ta biyo bayan zaben jihar Osun da kuma fuskantar zabe na 2019 da ake yi

- Ya ce hanyar farko da za a bi don kawo karshen matsalar shine kawo karshen talauci

Sanatan mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai ta kasa, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa akwai hanyoyi 6 da ya kamata abi matukar ana so a kawo karshen matsalar saye da sayar da kuri'u a yayin da ake gudanar da zabe a kasar.

Shehu Sani ya bayyana hanyoyin a shafinsa na Twitter, a ranar Juma'a 28 ga watan Satumba, inda ya ce mafi grima daga cikin hanyoyin kawo karshen saye da sayar da kuri'u shine kawo karshen talaucin da jama'a suke ciki, domin da yawa kan iya sayar da kuri'unsu dkn samu abun da zai ciyar da iyalansa.

Wannan shawarar ta Sani ta biyo bayan rahotannin da aka samu a na cafke mutane da dama a zaben gwamnan jihar Osun zagaye na biyu da aka kammala a jiya Alhamis, da kuma fuskantar zabe na 2019 da ake yi.

KARANTA WANNAN: Saraki: Zaben jihar Osun zagaye na biyu cin fuska ne ga demokaradiyya a Nigeria

Shehu Sani: Hanyoyi 6 na kawo karshen saye da sayar da kuri'u a wajen zabe

Shehu Sani: Hanyoyi 6 na kawo karshen saye da sayar da kuri'u a wajen zabe
Source: Depositphotos

Comrade Shehu ya ce hanyar farko da za a bi don kawo karshen matsalar shine kawo karshen talauci, daga nan kuma sai samar da shiri na musamman na tallafawa mutane da kudade, na ukkun su kuwa hukunta duk wanda aka cafke da aikata munanan laifuka.

Ya ce: "Mataki na hudu da za abi shine samar da wata hukuma da zata jibinci laifukan zabe da kuma dangogin karya dokokin zabe, bayan wannan kuma sai samar da wani shiri na musamman da za a rinka wayar da kan jama'a dangane da illolin siyasar kudi"

Sanatan ya bayyana bullo da tsarin kwarmato na masu sayen kuri'u a matsayin hanya ta shida da za a bi don kawo karshen saye da sayar da kuri'u, yana mai fatan cewa za a yi amfani da hanyoyin don ganin an gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel