Yanzu Yanzu: Ýar majalisar wakilai Funke Adedoyin ta mutu

Yanzu Yanzu: Ýar majalisar wakilai Funke Adedoyin ta mutu

Allah yayi wa wata ýar majalisar Najeriya rasuwa, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Funke Adedoyin ta kasance mamba a majalisar wakilai daga jihar Kwara, ta rasu a ranar Juma’a , 28 ga watan Satumba a babban birnin tarayya Abuja. Ta rasu tana da shekaru 54 a duniya.

Mista Atunwa, shugaban kwamitin shari’a a majalisa kuma dan takarar gwamna a jihar Kwara, yace Misis Adedoyin ta mutu bayan tayi fama da ciwon daji wato kansa.

Yanzu Yanzu: Ýar majalisar wakilai Funke Adedoyin ta mutu

Yanzu Yanzu: Ýar majalisar wakilai Funke Adedoyin ta mutu
Source: Twitter

Adedoyin ta yi a matsayin ministar lafiya a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tsakanin 1999-2003.

KU KARANTA KUMA: Zaben Osun: Adeleke ya sha alwashin zuwa kotu

Ta kasance daga cikin mambobin majalisa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da suka sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a farkon shekarar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel