2019: Buhari ya ci zabe ya gama – Gwamna Bindow

2019: Buhari ya ci zabe ya gama – Gwamna Bindow

Gwamna Mohammed Bindow na jihar Adamawa a ranar Juma’a, 28 ga watan Satumba ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na da kyawawan dama na lashe zaben shugaban kasa a 2019.

Gwamnanya bayyana hakan bayan ya kammala jefa kuri’a a zaben fidda gwani na shugaban kasa na ja’iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin Kolere dake karamar hukumar Mubi ta arewa dake Adamawa, kamfanin dilancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa ya kuma bayyana ayyukan cigaba da gwamnatinsa yi wanda ke nuni karara da cwar Buhari ya cancanciyin tazarce.

2019: Buhari ya ci zabe ya gama – Gwamna Bindow

2019: Buhari ya ci zabe ya gama – Gwamna Bindow
Source: Depositphotos

Bindow ya kuma bayyana cewa zaman lafiya da ya wanzu aankin arewa maso gabas na daya daga ciin nasarorin gwamnatin shugaba Buhari.

Ya nuna farin ciki da gamsuwa da tarin mambobin APC da suka halarci zaben da kuma zaman lafiya da gudana wajen.

Gwaman ya kuma nuna karfin gwiwar cewa zaben fidda gwani masu zuwa zasu kasance cikin lumana sannan y bukaci magoya baya da su ci gaba da hakuri. An rahoto cewa gwamnan yayi zabe ne da rana.

Gwnan ya kuma lura da wasu cibiyoyin zabe a kananan hukumomin Mubi ta Arwa da na Kudu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Abdul’aziz Yari na jihar Zamfara ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci a sake zabarsa a karo na b iyu sannan kuma yana bukatar goyon bayan dukkanin yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Zaben Osun: Adeleke ya sha alwashin zuwa kotu

Yari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayinda yake jagwabi ga magoya bayan jam’iyyar Progressives Congress (APC) a mazabar Abubakar Tunau Model Primary School a garin Talata-Mafara, karamar hukumar Talata-Mafara dake jihar.

Gwamnan yace Shugaba Buhari ya cancanci goyon bayan dukkanin ýan Najeriya, ba tare da la’akari da jam’iyy ba idan aka yi duba ga kyakyawar kudirinsa na sun ganin ci gaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel