Da duminsa: Bayan barazanar Wike, PDP zata gudanar da taron gangaminta a Fatakwal

Da duminsa: Bayan barazanar Wike, PDP zata gudanar da taron gangaminta a Fatakwal

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yanke shawaran gudanar da taron gangaminta na zaben dan takaran shugaban kasa a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Wannan labari ya bayyana ne bayan taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar da ya gudana a yau Juma’a. 28 ga watan Satumba, 2018 a hedkwatan jam’iyyar da ke birnin tarayya, Abuja.

Jam’iyyar ta bukaci ganawa ne bayan barazanar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike yayi na cewa zasu koyawa PDP hankali idan aka dauke taron daga jihar Ribas.

Wasu yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar sun kai korafinsu na rashin amincewa da jihar Ribas matsayin wajen gudanar da taron gangamin.

Da duminsa: Bayan barazanar Wike, PDP zata gudanar da taron gangaminta a Fatakwal

Da duminsa: Bayan barazanar Wike, PDP zata gudanar da taron gangaminta a Fatakwal
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya caccaki wasu yan takaran kujeran shugaban kasa daga Arewa wadanda suka nuna rashin yardansu kan shirya taron gangamin jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) a garin PortHarcourt, jihar Ribas.

Ya bayyana cewa wadannan yan takara makiya jihar Ribas ne kuma Neja Delta ga baki daya. Za’a gudanar da taron gangamin ne ranan 5 da 6 ga watan Oktoba 2018.

KU KARANTA: Hotuna: Yadda zaben kato bayan kato ya gudana a jihar Kano

Duk da cewa wasu daga cikin yan takaran 13 basu da matsala da gudanar da taron a Ribas, wasu sun nuna rashin amincewansu da wannan abu.

Wike ya ce yan takaran sun fara saba alkawuransu na cewa zasu tabbatar da garambawul idan suka ci zabe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel