Saraki: Zaben jihar Osun zagaye na biyu cin fuska ne ga demokaradiyya a Nigeria

Saraki: Zaben jihar Osun zagaye na biyu cin fuska ne ga demokaradiyya a Nigeria

- Saraki ya ce zaben jihar Osun da aka gudanar zagaye na biyu babban cin fuska ne ga demokaradiyya a Nigeria

- Ya ce zaben kaface kawai da jam'iyar APC ta yi amfani da ita wajen yin magudin zabe

- A cewar Saraki an gudanar da zaben ne cike da yad'a kalaman karya dana barazana, hadi da cin zarafin

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki ya ce zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar zagaye na biyu babban cin fuska ne ga demokaradiyya a Nigeria, bayan da wasu daga cikin masu sa ido a gudanar da zaben suka nuna rashin ingancinsa saboda rikie-rikicen da aka samu a ranar zaben.

A cikin wata sanarwa daga hannun Yusuph Olaniyonu, mai magana da yawunsa, Saraki ya ce zaben gwamnan jihar zagaye na biyu kaface kawai da jam'iyar APC ta yi amfani da ita wajen yin magudin zabe.

Ya zargi jam'iyya mai mulki ta razanar da jama'a ta hanyar yad'a labaran karya da kuma yi masu barazana, kana ya bukaci jama'ar garin da su yi hakuri akan wannan makircin murdiyar zaben "saboda babu wanda ya isa ya kwace nasara".

Saraki: Zaben jihar Osun zagaye na biyu cin fuska ne ga demokaradiyya a Nigeria

Saraki: Zaben jihar Osun zagaye na biyu cin fuska ne ga demokaradiyya a Nigeria
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: KARIN BAYANI: Gwamnati ta sanya dokar ta baci a garuruwan Jos

"A jiya dai munga yadda aka tauye hakkin jama'ar jihar Osun a zagaye na biyu na zaben gwamnan jihar Osun. An gudanar da zaben ne cike da yad'a kalaman karya dana barazana, hadi da cin zarafin mutane. Kwararrun masu saka ido a zaben sun tabbatar da cewa an hana jama'a kad'a kuri'a a wasu rumfunan zabe, ta hanyar amfani da 'yan ta'adda," a cewar sanarwar.

"Kamar yadda na bayyana kwanakin baya, an shirya wannan zaben zagaye na biyu kawai don APC ta samu kofar yin murdiya a sakamakon zaben. Irin wannan zaben cin fuska ne ga demokaradiya da kuma zama izina ga hukumomi ko kungiyoyin da ke kare rajin 'yan Nigeria da ake kwace masu a wajen zabe.

"Lamarin zai zama abun mamaki matuka, sanin cewa a zaben farko jam'iyyun na tafiya kunnen doki, inda PDP ta gota APC da kuri'u 353, amma bayan kwanaki 4, INEC ta saki wani sakamakon san zuciyarsa, wanda hankali ma ba zai dauka ba."

A dai-dai wannan gabar, shugaban majalisar dattijai ya yi kira da sa bakin kasashen ketare, yana mai cewa bai kamata a canja irin tsarin da aka gudanar da zaben 2015 ba, "idan kuwa ba a gaggauta yin hakan ba, to kuwa zaben 2019 ma zai kasance kamar zaben jihar Osun."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel