Zaben Osun: Adeleke ya sha alwashin zuwa kotu

Zaben Osun: Adeleke ya sha alwashin zuwa kotu

Sanata Ademola Adeleke, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Osun, ya sha alwashin yin amfani da karfi da doka wajen ganin ya sauya akalar sakamakon zaben zuwa gare shi.

Adeleke, wanda ya dauki wannan alwashin a lokacin zantawarsa na farko bayan zaben a ranar Juma’a a Ede, Osun ya yabama yan Najeriya da mambobin labarai kan gudunmawar da suka bayar wajen goyon bayan damokradiyya.

Ya yi zargin cewa anyi masa fashi a mazabu , inda ya ba da tabbacin cewa za’ayi kokarion ganin an dawo da sakamakon zaben.

Zaben Osun: Adeleke ya sha alwashin zuwa kotu

Zaben Osun: Adeleke ya sha alwashin zuwa kotu
Source: Depositphotos

Dan takarar na PDP ya bukaci mutane da kada su bari a sace masu gwiwa, inda ya kara da cewa nasarar da akayi akansu na dan lokaci ne zai dawo gare su daga baya.

Adeleke ya kara da cewa ya zama dole mutanen Osun so zamo masu sanya idanu sosai amma su kwantar da hankalinsu.

KU KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani na APC: Buhari ya cancanci zango na biyu – Gwamna Yari

Haka zalika shugaba PDP a Osun, Hon. Soji Adagunodo yayi zargin cewa anyi magudin zaben sannan aka bi shi da rikici.

A ranar Alhamis ne hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da Alhaji Gboyega na jam’iyyar All Progressives Party(APC) a matsayin wanda yayi nasara a zaben da aka sake gudanarwa bayan an dage zaben daga ranar 22 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel