ASUU tace Gwamnati ta saba yarjejeniyar da aka yi Jami’o’i a 2017

ASUU tace Gwamnati ta saba yarjejeniyar da aka yi Jami’o’i a 2017

Mun samu labari cewa Kungiyar Malaman Jami’a na ASUU tayi kira ga Gwamnatin Tarayya ta biya su kudin su Naira Tiriliyan 1.1 da aka tsara domin gyara Makarantun Jami’o’i a fadin kasar a cikin shekaru 6 da su ka wuce.

ASUU tace Gwamnati ta saba yarjejeniyar da aka yi Jami’o’i a 2017

Bukatar Jami’o’in Najeriya ta fi karfin Biliyan 20 Inji ASUU
Source: UGC

Yanzu haka dai Kungiyar ta fara kira ga Malaman Jami’a su tafi yajin aiki a fadin kasar nan. Shugaban Kungiyar na Yankin Filato Farfesa Lawan Abubakar ya nuna wannan lokacin da ya zanta da manema labarai jiya.

Yankin na Jos din ya kunshi Jami’o’in Abubakar Tafawa Balewa na Bauchi da Jami’ar Tarayya ta Kashere a Jihar Gombe da ta Jos; da kuma Jami’ar Jihar Filato da ke Jihar Bokkos inji Shugaban na ASUU Lawan Abubakar.

KU KARANTA: Babu wani titi da PDP ta gina tsawon shekaru 16 - Shugaba Buhari

Kungiyar ta kuma musanta cewa Gwamnatin Tarayya ta aiko mata da Biliyan 20. Abubakar yace abin da Jami’o’in Najeriya 64 da ake da su su ke nema ya haura Tiriliyan guda don haka babu abin da Biliyan 20 za ma tayi masu.

A baya an yi wa Jami’o’i alkawarin Biliyan 220 kowace shekara. A dalilin hakane ASUU ta ke neman a ba ta Tiriliyan 1.1. Malaman Jami’ar sun nuna cewa ba su gamsu da tattaunawar da ake yi da Gwamnati na karin albashi ba.

Dazu kun ji cewa Shugaban ASUU na Yankin Legas watau Farfesa Olusiji Sowande yayi karin haske game da batun cewa Gwamnatin Tarayya ta aiko mata da makudan kudin da ta ke bi bashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel