Zaben fidda gwani na APC: Buhari ya cancanci zango na biyu – Gwamna Yari

Zaben fidda gwani na APC: Buhari ya cancanci zango na biyu – Gwamna Yari

Gwamna Abdul’aziz Yari na jihar Zamfara ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci a sake zabarsa a karo na b iyu sannan kuma yana bukatar goyon bayan dukkanin yan Najeriya.

Yari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayinda yake jagwabi ga magoya bayan jam’iyyar Progressives Congress (APC) a mazabar Abubakar Tunau Model Primary School a garin Talata-Mafara, karamar hukumar Talata-Mafara dake jihar.

Zaben fidda gwani na APC: Buhari ya cancanci zango na biyu – Gwamna Yari

Zaben fidda gwani na APC: Buhari ya cancanci zango na biyu – Gwamna Yari
Source: Depositphotos

Gwamnan yace Shugaba Buhari ya cancanci goyon bayan dukkanin ýan Najeriya, ba tare da la’akari da jam’iyy ba idan aka yi duba ga kyakyawar kudirinsa na sun ganin ci gaban kasar.

A cewarsa, lokacin da Buhari ya zamo shugaban kasar Najeriya a 2015, ya hadu da kalubale da dama da bai taba zato ba, amma a dan kankanin lokaci ya yi yunkuri don magance su.

Gwamnan ya bukaci mutanen jihar da su ci gaba da kwantar da hankalinsu sannan su cigaba da marawa gawamnati baya wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NPS ta sallami jami’ai 3 kan safarar wasu haramtattun kayayyaki da ka iya barazana ga tsaro a gidan yari

Ya kuma bukaci matasa das u rungumi zaman lafiya domin korma duk wani rikici da dabanci da sunan siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel