Gwamnatin Tarayya ta amince da $64m don samar da wuta a wasu yankunan karkara masu mai

Gwamnatin Tarayya ta amince da $64m don samar da wuta a wasu yankunan karkara masu mai

- FEC ta amince da fitar da dala miliyan 64.2 domin samar da wutar lantarki a wani yankin jihar Delta

- Gwamnatin tarayya ta bada tabbacin cewa ambaliyar ruwa tazo karshe

- Za'a kammala aikin samar da wutar lantarkin ne a shekara 4 ko biyar masu zuwa

Gwamnatin Tarayya ta amince da $64 don samar da wuta a wasu yankunan karkara masu mai

Gwamnatin Tarayya ta amince da $64 don samar da wuta a wasu yankunan karkara masu mai
Source: Depositphotos

Kwamitin zababbu na tarayya a ranar laraba ya yarje da fitar da dala miliyan 64.2 domin samar da wutar lantarki a wasu yankuna na jihar Delta.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ambaliyar ruwa tazo karshe domin kuwa ruwa a Cameroun na raguwa.

Karamin ministan man fetur ne yayi bayani ga manema labarai a fadar shugaban kasa, Dr. Ibe Kachikwu, yace zanga zangar lumanar da mazauna yankin suka dinga tasa Gwamnatin tarayya ta zartar da hakan.

DUBA WANNAN: Fin rabin Tiriliyan na naira muke bin gwamnati, masu shigo da mai

Kamar yadda yace, yankunan sun tambayi dalilin da yasa za'a kwashe kashi 50 na gas daga yankin a kai shi wasu wuraren da basu da wutar lantarki. Matatar man fetur ta kashe Naira miliyan 18 domin samar da man na'urar dake bada wutar lantarki a yankunan.

Da amincewar FEC na samar da wuta lantarki ta dindindin ga yankunan, zai kawo karshen matsalolin wutar su nan da shekaru 4 zuwa 5.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel