Da dumi-dumi: Jirage biyu sunyi hatsari a Abuja

Da dumi-dumi: Jirage biyu sunyi hatsari a Abuja

Jiragen sama mallakar sojin saman Najeriya guda biyu sunyi hatsari sakamakon karo da juna da su kayi a babban birnn tarayya Abuja.

Hatsarin ya afku ne a kusa da garin Katampe da ke babban birnin tarayya Abuja a yayin da matukan jiragen ke shirye shirye bukukuwar ranar saman 'yancin Najeriya karo na 58.

An tabbatar da cewa matukan ba su mutu ba saboda anyi amfani da na'urar parachute an ciro su kafin jirgin ta kama da wuta.

Da dumi-dumi: Jirage biyu sunyi hatsari a Abuja

Da dumi-dumi: Jirage biyu sunyi hatsari a Abuja
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: Kusoshin jam'iyyar PDP za suyi wata ganawar gagawa

Kakakin hukumar sojin saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola ya tabbatar da afkuwar hatsarin a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai.

"Ina son in tabbatar da cewa wasu jiragen samu biyu mallakar NAF sunyi hatsari yayin da suke atisaye na shirye-shiryen bukin zagayowar ranar 'yancin Najeriya karo na 58. A saurari karin bayani anjima," inji shi.

Ku biyo mu domin karin bayan...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel