Buhari ya tattauna da yan Najeriya mazauna kasashen waje bayan sun karrama shi

Buhari ya tattauna da yan Najeriya mazauna kasashen waje bayan sun karrama shi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da tawagar yan Najeriya mazauna kasashen waje a kasar Amurka, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi gida Najeriya da hanyoyin ciyar da kasar gaba.

Legit.ng ta ruwaito Buhari yayi wannan ganawar ne bayan kammala taron koli na majalisar dinkin duniya daya gudana babban ofishin majalisar dake kasar Newyork ta kasar Amurka.

KU KARANTA: Musulmai ma fuskantar tsangwama, kyara da cin fuska a nahiyar turai – Bincike

Buhari ya tattauna da yan Najeriya mazauna kasashen waje bayan sun karrama shi

Buhari da yan Najeriya
Source: Facebook

Daga cikin wadanda suka raka Buhari wannan taro akwai ministar harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki da kuma mashawarciyar shugaban kasa akan harkokin kasashen waje, Abike Dabiri Erewa.

A yayin tattaunawar tasu, Buhari ya bayyana ma yan Najeriya cewa shi kadai ne dan takarar shugaban kasa a Najeriya saboda sauran abokan takarartasa sun koma jam’iyyar adawa, “Amma zan bi su har can don na kadasu a zabe mai zuwa.” Inji shi.

Haka zalika yan Najeriyan sun karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da shaidar jinjina da majalisar dokokin kasar Amurka ta baiwa tawagar da yan Najeriya da suka lashe gasar tseren kankara a karkashin jagorancin Seun Adigun.

Buhari ya tattauna da yan Najeriya mazauna kasashen waje bayan sun karrama shi

Buhari da Seun
Source: Facebook

Bugu da kari mataimakin maigarin birnin New York wanda dan asalin Najeriya ne, Ugo Nwakoro ya karrama shugaba Buhari da lambar yabo, sa’annan Buhari ya mika godiyarsa da dukkansu, inda yayi kira garesu da su cigaba da zama yan kasa nagari abin koyi.

A yayin wannan taro na majalisar dinkin duniya karo na saba’in da uku shugaban kasa ya karbi bakoncin shugaban kungiyar kasashen musulmai ta duniya, Sheikh Othaimeen, shugaban kasar Ghana Nana Akufo, shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa da shugaban majalisar dinkin duniya Antonio Gutteres.

Buhari ya tattauna da yan Najeriya mazauna kasashen waje bayan sun karrama shi

Buhari da mataimakin maigarin New York
Source: Facebook

Buhari ya tattauna da yan Najeriya mazauna kasashen waje bayan sun karrama shi

Taron
Source: Facebook

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel