Kamfunna 19 ne ke neman sayen Lantarkin arewa maso gabas

Kamfunna 19 ne ke neman sayen Lantarkin arewa maso gabas

- Kamfanoni 19 suka nuna bukatar siyan kamfanin wuta lantarki na Afam da YDC

- A cikin kamfanonin da suka nuna bukatar mallakar kamfanin akwai sanannu a masana'antar lantarki

- Duk da na siyar da kamfanin wutar lantarki ta Yola, rashin tsaro yasa ya dawo hannun Gwamnatin tarayya

Kamfunna 19 ne ke neman sayen Lantarkin arewa maso gabas

Kamfunna 19 ne ke neman sayen Lantarkin arewa maso gabas
Source: UGC

Masana'antu 19 ne suka bayyana bukatar mallakar kamfanin wutar lantarki na Afam da kuma kamfanin raba wutar lantarki na Yola (YDC) da Gwamnatin tarayya ta daga don siyarwa.

Kusa da rufe karbar bukatar siyan kamfanonin, kamfanoni 7 suka bayyana bukatar siyan Afam, sai 12 kuma suka bayyana bukatar mallakar kamfanin wutar lantarki na Yola.

Shugaban sadarwa ta Bureau of Public Enterprises (BPE), Amina Othman Tukur, tace a cikin kamfanonin akwai sanannu a masana'antar wutar lantarki.

DUBA WANNAN: Sultan ya koka kan matsalolin kasar nan

Idan za a tuna, kamfanin raba wutar lantarki na Yola an siyar dashi a 2013 ga masu hannayen jari, matsalar tsaro a yankin arewa maso gabas yasa ya koma hannun Gwamnatin tarayya. Shi kuwa Afam yayi jinkirin saka hannu ne a yarjejeniyar shi tsakanin GSAA da GTA.

A 2017 ne National Council on Privatisation (NCP) ta bada goyon bayan siyar da kamfanonin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel