Kungiyar 'Kwadago ta hana Jirage tashi a Filin Jirgin sama na jihar Legas

Kungiyar 'Kwadago ta hana Jirage tashi a Filin Jirgin sama na jihar Legas

Da sanadin shafin jaridar The Sun mun samu cewa da sanyin safiyar yau ta Juma'a, jami'an kungiyar kwadago ta Najeriya sun mamaye harabar filin jirgin sama na jihar Legas tare da hana Jirage keta hazo domin safarar Fasinjoji.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun da misalin karfe 6.30 na safiyar yau ta Juma'a, ma'aikatan kungiyar suka yiwa filin jirgin saman kawanya tare da hana ma'aikatan wasu kamfanonin jiragen sayarwa da fasinjoji tikitin su.

Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar ta yi wannan yunkuri domin jaddada tsanani na yajin aikin da ta shiga a ranar Alhamis din da ta gabata, inda ma'aikatu da dama dake fadin kasar nan suka ajiye ayyukan su.

Kungiyar 'Kwadago ta hana Jirage tashi a Filin Jirgin sama na jihar Legas

Kungiyar 'Kwadago ta hana Jirage tashi a Filin Jirgin sama na jihar Legas
Source: UGC

Kamar yadda jaridar ta The Sun ta ruwaito, akwai kamfanonin jiragen sama musamman na Arik Air da Air Peace da tuni suka riga da sayar da tikitin su ga fasinjoji masu sammakon tafiya ta sassafiya.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna za ta wallafa Sunayen Wakilai 2, 677 da za su fidda gwanayen Takara a 2019

Sai dai wannan lamari na kungiyar kwadago ya jefa fasinjojin cikin tsaka mai wuya tare da shiga cikin halin kaka nikayi na rashin samun tafiya wuraren da suka nufata.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban ma'aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, ya gana da shugabannin kungiyar kwado a fadar Villa domin tattauna batutuwan da suka shafi bukatar kungiyar na tabbatar da sabon mafi karancin albashin ma'aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel