Ma'aikata sun maka kamfanin Unilever a kotu

Ma'aikata sun maka kamfanin Unilever a kotu

- Akalla ma'aikata 10 daga kasar Kenya suka maka kamfanin Unilever a gaban kotun kuliya da ke kasar Landan

- Rikicin da ya barke a bayan zaben 2007 na kasar ya janyo asarar rayukan mutane sama da dubu daya

- Sai dai kamfanin ya ce ya bai wa kowane ma'aikaci hakkinsa da duk wani taimako da ya ke bukata a lokacin rikicin

Akalla ma'aikata 10 daga kasar Kenya suka maka kamfanin Unilever na kasashen Holland da Burtaniya a gaban kotun kuliya da ke kasar Landan, sakamakon gazawar kamfanin na sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, musamman na kare hakkin ma'aikatan kamfanin dama hakkin dan adam a rikicin da ya barke bayan shekara ta 2007.

A cewar ma'aikatan, kamfanin Unilever ya yi biris da nuna halin ko-oho wajen daukar matakan kare rayukansu a wancan lokacin, zargin da shi kuma kamfanin Unilever ya karyata.

Rikicin da ya barke a bayan zaben 2007 na kasar ya janyo asarar rayukan mutane sama da dubu daya, tare da raba dubunnai da gidajensu.

KARANTA WANNAN: Dakile ta'addanci: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a jihar Kwara

Ma'aikata sun maka kamfanin Unilever a kotu

Ma'aikata sun maka kamfanin Unilever a kotu
Source: Twitter

A yayin da suke shigar da karar a gaban kotu, ma'aikatan sun ce akalla ma'aikatan kamfanin 7 ne suka mutu daga cikin wadanda aka kashe, sannan an yiwa mata akalla 56 fyade a lokacin rikicin.

Rahotanni daga BBC na cewa ma'aikatan sun ce shuwagabannin gudanarwar kamfanin na Kenya, sun jefa rayuwarsu cikin mummunan hatsari daga barazanar mutuwa bayan da ma'aikatan suka shigar da wannan korafi nasu a kotu.

Sai dai a bangaren Unilever, kamfanin ya ce ya bai wa kowane ma'aikaci hakkinsa da duk wani taimako da ya ke bukata a lokacin rikicin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel