Da duminsa: Kusoshin jam'iyyar PDP za suyi wata ganawar gagawa

Da duminsa: Kusoshin jam'iyyar PDP za suyi wata ganawar gagawa

A jiya, Juma'a ne jam'iyyar PDP ta kira mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar zuwa wata taron gagawa domin su tattauna a kan jihar da za'a gudanar da babban taro na kasa da jam'iyyar ke shirin yi.

Idan ba'a manta ba, jam'iyyar ta yanke shawarar gudanar da taron gangamin a ranar 6 ga watan Oktoba a jihar Rivers sai dai wasu daga cikin mambobin jam'iyyar ba su amince da hakan ba.

Da duminsa: Kusoshin jam'iyyar PDP za suyi wata ganawar gagawa

Da duminsa: Kusoshin jam'iyyar PDP za suyi wata ganawar gagawa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Siyasar Kano: Lado ya janyewa Shekarau takarar Sanatan Kano ta Tsakiya

Hakan ne ya sa, Ciyaman din Kwamitin amintatu na jam'iyyar, Sanata Walid Jibrin ya kira taron kwamitin masu gudanarwa na jam'iyyar domin a sake tattaunawa da kuma amincewa a kan wajen da za'a gudanar da babban taron.

Kwamitin za ta cimma matsaya guda bayan kammala taron da jiga-jigan jam'iyyar.

Ku cigaba da biyo mu domin karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel