Fitar da 'yan takara: APC ta nada gwamnoni a matsayin jami'an zabe

Fitar da 'yan takara: APC ta nada gwamnoni a matsayin jami'an zabe

- Jam'iyyar APC ta zabi gwamnonin jihohi su kasance masu sanar da sakamakon zabe a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar

- Sanarwan ta fito ne daga bakin Sakataren yada labarai na riko na jam'iyyar, Yekini Nabena

- Za'a gudanar da zabukan fidda gwanin ne a dukkan jihohin Najeriya da kuma babban birnin tarayya, Abuja

Kwamitin gudanarwa na All Progressives Party (APC) ta zabi gwamnonin jihohi a matsayin jami'an zabe da za su sanar da sakamakon zabukan fitar da gwani na shugabancin kasa da za'ayi a jihohinsu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewar za'a gudanar da zabukkan fidda gwanin ne a yau Juma'a 28 ga watan Satumba a babban birnin tarayya Abuja da kuma sauran jihohin Najeriya.

Gwamnonin APC ne za su kasance baturen zabe a zaben fidda gwani na shugaban kasa

Gwamnonin APC ne za su kasance baturen zabe a zaben fidda gwani na shugaban kasa

DUBA WANNAN: Siyasar Kano: Lado ya janyewa Shekarau takarar Sanatan Kano ta Tsakiya

Legit.ng ta gano cewa Sakataren yada labarai na riko na jam'iyyar, Yekini Nabena ne ya bayar da wannan sanarwar a daren jiya Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.

Ya kuma ce a jihohin da APC ba ta da gwamnoni, Sanatoci da Ministocin da ke wadannan jihohin ne za su yi aiki a matsayin masu sanar da sakamakon zabukkan.

Ya kara da cewa 'yan majalisar wakilai na tarayya da na jihohi suma za su taimaka wajen sanya idanu a kan zabukan da mazabansu.

Za'a gudanar da zaben fitar da gwanin ne saboda a samu amincewar dukkan 'yan jam'iyyar game da takarar shugaba Muhammadu Buhari a matsayinsa na dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel