Uwargidar shugaban kasa ta samu babbar lambar yabo a kasar Amurka

Uwargidar shugaban kasa ta samu babbar lambar yabo a kasar Amurka

Uwargidar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ya samu lambar yabo a kasar Amurka sakamakon taimako da take baiwa mata musamman wadanda ake safararsu ko kum cin zarafinsu, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata cibiyar kasar Amurka ‘Global Empowerment Movement Corporation, U.S.’ ce ta karrama Aisha da lambar yabo na duniya gaba daya bisa tallafin da take baiwa mata tare da inganta rayuwarsu.

KU KARANTA: Musulmai ma fuskantar tsangwama, kyara da cin fuska a nahiyar turai – Bincike

Sai kuma gwamnatin jahar Geogia data karrama Aisha da shaidar zaman yar jahar, tare da lambar yabo na girmamawa, sakamakon kare hakkin mata da take yi a Najeriya. An mika ma Aisha kyautukan ne a gidan Najeriya dake birnin New York.

Shugaban cibiyar, Blessing Itua tace sun yaba da kokarin da Aisha take yi na inganta rayuwar mata ta kungiyarta mai suna ‘Future assured. “Ta wannan cibiya Aisha Buhari ta shirya tsare tsare da dama don tallafa ma mata da yan mata, kuma hakan ya inganta rayuwarsu da dama.

“Ta wannan cibiya, Aisha na taimaka ma mata ta bangaren ilimi, tallafi da kuma kyautata rayuwarsu, haka zalika tana yaki da safarar mata, cin zarafinsu, kuntata musu, da kuma fyade wanda hakan yayi daidai da kudurin gwamnatin Najeriya.” Inji ta.

Da take amsan kyautukan, Uwargida Aisha ta gode ma kungiyoyin da suka fahimci ta cancanci wadannan kyautka musamman a kokarinta na kwatar ma mata hakkokinsu ta cibiyarta ‘Future assured.”

“Abindake bani kwari gwiwa shine halin da mata suke ciki na rayuwar kunci a duk fadin duniya, don haka ne na daukar ma kaina alkawarin zan yi iya bakin kokarina dn ganin na taimaki duk wata mace dake cin kunci da fatan hakan zai rage faruwarsu

“Fatana shine mata su gane damanmakin da suke dasu da zasu inganta rayuwarsu, tare da samun tabbacin zasu samu kariya a tsakanin jama’a. na sadaukar da wadannan kyautuka ga duk matan dake gwagwarmaya a rayuwarsu don yaki da cutar da mata da kuma inganta rayuwa.” Inji ta

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel