Jam’iyyar APC ta canza ranar da za ta fitar da ‘Yan takarar Gwamna a Najeriya

Jam’iyyar APC ta canza ranar da za ta fitar da ‘Yan takarar Gwamna a Najeriya

- Jam’iyyar APC ta canza ranar da za a tsaida Gwamnonin Jihohi

- Za ayi zaben ne a Ranar 30 ga watan nan a maimakon Ranar 29

Jam’iyyar APC ta canza ranar da za ta fitar da ‘Yan takarar Gwamna a Najeriya

APC ta canza ranar ba ‘Yan takarar Gwamnoni tuta
Source: Depositphotos

Mun samu labari jiya cewa Jam’iyyar APC da ke mulkin Kasar nan ta sake canza ranakun da za ta fitar da ‘Yan takarar ta da za su rike mata tuta a zabe mai zuwa na 2019 idan har lokaci yayi. A baya dai an ta sauya jadawalin zaben.

Mukaddashin Sakataren yada labarai na Jam’iyyar ta APC watau Yekini Nabena ne ya bayyana wannan jiya. Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan Majalisar NWC da ke da wannan hurumi tayi la’akari da wasu abubuwa.

KU KARANTA: Masu ganin cin ta a 2019 sun bar APC kuma za mu hadu a filin zabe – Buhari

Jam’iyyar ta canza ranar da za tayi zaben fitar da gwani ne na Gwamnonin Jihohi inji babban Jami’in na ta Yekini Nabena. Jam’iyyar ta bayyana cewa sauran zabukan su na nan a ranakun da aka tsara ba tare da an sauya ba.

Yanzu dai za ayi zaben tsaida ‘Yan takarar Gwamna ne a Ranar 30 ga wannan watan a maimakon Ranar 29 da aka tsaida a baya. Za kuma ayi zaben masu harin kujerar Sanatoci ne a Ranar 2 ga watan Oktoba idan Allah ya kai mu.

APC dai za ta tsaida wanda za ta ba tutar tafiya Majalisar Tarayya ne a Ranar 3 ga watan gobe inda za ayi na ‘Yan Majalisun Jihohi a kashegarin ranar. A Ranar 6 ga wata ne kuma Jam’iyyar za ta tsaida 'Dan takarar Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel