2019: kwamitin tantance yan takara ta watsar da ministocin Buhari 2, 3 sun sha

2019: kwamitin tantance yan takara ta watsar da ministocin Buhari 2, 3 sun sha

Daga cikin ministoci masu ci a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, an samu guda uku da suka tsallake matakin tantance yan takarkarun gwamna, sa’annan an samu guda biyu da basu tsallake tantancewar ba saboda wasu matsaloli.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito uwar jam’iyyar APC ce ta sanar da haka ta cikin wata sanarwa data fitar dake dauke da jerin sunayen yan takarkarunta da kwamitin tantance yan takara ta tabbatar dasu akan cewa sun cancanci tsayawa takara a zaben shekarar 2019.

KU KARANTA: Yajin aiki: Zamu hana jiragen sama sauka da tashi daga Najeriya – Kungiyar kwadago

2019: kwamitin tantance yan takara ta watsar da ministocin Buhari 2, 3 sun sha

Ministoci
Source: UGC

An bayyana sunayen ministocin da suka tsallake wannan mataki kamar haka; Usani Usani, ministan Nej Delta, Mansur Ali, ministan tsaro da kuma Mustapha Baba Shehuri karamin ministan ayyuka, lantarki da gidaje.

Ministan Neja Delta Usani na muradin zama gwamnan jahar Kros Ribas ne, yayin da Baba Shehuri ke muradin zama gwamnan jahar Borno, sai kuma shi Masur Dan Ali dake ganin ya dare mukamin gwamnan jahar Zamfara wanda hakan yasa a yanzu haka basa ga maciji da gwamnan jahar Abdul Aziz Yari.

2019: kwamitin tantance yan takara ta watsar da ministocin Buhari 2, 3 sun sha

Ministoci
Source: UGC

Sai kuma ministocin da suka gagara tsallake wannan mataki da suka hada da ministan sadarwa Adebayo Shittu da yan takarar gwamna daya tilo daga jam’iyyar APC, Aisha Alhassan da aka fi sani da Maman Taraba, ministan al’amuran mata.

Mama Taraba na neman tsayawa takarar gwamnan jahar Taraba ne, yayin da Adebayo Shittu ke son tsayawa takarar gwamnan jahar Oyo, sai da kwamitin ta bayyana dalilin rashin amincewa da Shittu shine saboda bai yi bautar kasa ba bayan ya kammala digirinsa na farko, amma basu bayyana dalilin yin watsi da Aisha Jummai ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel