Bashin Biliyan 20: Kungiyar ASUU ta karyata Gwamnatin Tarayya

Bashin Biliyan 20: Kungiyar ASUU ta karyata Gwamnatin Tarayya

- Gwamnati tayi ikirarin biyan ASUU kudi har Naira Biliyan 20

- Shugaban Kungiyar na Legas ya karyata Gwamnatin Tarayya

- ASUU tace har yanzu ma dai su na biyan Gwamnati tarin bashi

Bashin Biliyan 20: Kungiyar ASUU ta karyata Gwamnatin Tarayya

ASUU tace Gwamnati ba ta aiko masu da wasu kudi ba
Source: Depositphotos

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust ta kasar nan cewa Kungiyar nan ta ASUU ta Malaman Jami’an Najeriya ta karyata maganar cewa Gwamnatin Tarayya ta aiko mata da makudan kudin da ta ke bi bashi kwanan nan.

Shugaban Kungiyar Malaman Jamu’an na Yankin Legas watau Farfesa Olusiji Sowande yayi karin haske game da labarin lokacin da ya zanta da ‘Yan jarida a tsakiyar makon nan. Sowande yace yaudarar Jama’a kurum Gwamnati ke yi.

KU KARANTA: An zare kudin da aka aikawa Jihar Benuwai domin biyan bashin albashi

Farfesa Sowande yace Gwamnatin Tarayya na kokarin gogawa Kungiyar ASUU bakin jini ne a idon jama’a don haka ta kawo maganar turawa Kungiyar Biliyan 20 a karshen bara. Shugaban na ASUU yace sam kudin bai zo hannun su ba.

Olusiji Sowande ya kara da cewa Gwamnati ta na ba Jami’o’i wannan kudi ne domin su amfana amma a hakikanin gaskiya ba ASUU ake turowa wannan kudi ba. Sowande yace yanzu haka ma dai ASUU na bin Gwamnati Biliyan 220.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel