Gwamnatin Tarayya ta gagara warware matsalolin kasar nan - Sultan

Gwamnatin Tarayya ta gagara warware matsalolin kasar nan - Sultan

- Sarkin musulmi ya fadi rashin son shawo kan matsalolin Najeriya ce matsalar Gwamnatin

- Ya bukaci yan Najeriya dasu bude baki su fadi matsalolin su

- Matsalolin kasar nan sun fara ne lokacin da aka jingine masarautun gargajiya

Gwamnatin Tarayya ta gagara warware matsalolin kasar nan - Sultan

Gwamnatin Tarayya ta gagara warware matsalolin kasar nan - Sultan
Source: Facebook

Shugaban majalisar koli ta addinin musulunci kuma Sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na uku, yace rashin son shawo kan matsalolin Najeriya ne yake kawo cikas ga Gwamnatin Najeriya.

Ya bukaci yan Najeriya dasu bude baki su fadi matsalolin dake damun su.

Sarkin musulmin ya fadi hakan ne a taron sarakunan gargajiya na yanki shida na kasar Najeriya da akayi a garin Jos a ranar Alhamis.

Ya tabbatar cewa dole mutane su koyi fadin matsalolin dake damun su saboda asan hanyar shawo kanta.

Kamar yanda ya fada, Idan akwai matsaloli, sarakunan gargajiya basu gujewa amma yan siyasa gudun hakan suke yi.

DUBA WANNAN: A kula da yaduwar makaman Nukiliya - Buhari ga Duniya

"Mu dena gujewa matsaloli, zai fi Idan muka zauna muka shawo kansu. Matsalolin kasar nan su fara ne lokacin da aka jingine masarautun gargajiya. Muna bada shawara ne domin cigaban kasar. Bama fadawa gwamnati tayi daidai ko ba daidai ba." inji Sarkin musulmi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel