Matatun mai sun durkushe warwas a makon nan har da kashi hudu bisa biyar

Matatun mai sun durkushe warwas a makon nan har da kashi hudu bisa biyar

- Rashin gyara matatun ma fetur ya jawo raguwar samar da kayayyakin man fetur da kashi 18

- Rahoton Lalacewar aiyukan matatun na kunshe ne rahoton kudi na karshen wata na matatar

-Samuwar fetur da kalanzir ya fadi daga lita miliyan 125.86 daga lita miliyan 153.37

Matatun mai sun durkushe warwas a makon nan har da kashi hudu bisa biyar

Matatun mai sun durkushe warwas a makon nan har da kashi hudu bisa biyar
Source: Facebook

DUBA WANNAN: A kula da yaduwar makaman Nukiliya - Buhari ga Duniya

Rashin gyara lalatattun matatun man fetur yasa Gwamnatin tarayya ta fuskanci raguwar samuwar kayayyakin man fetur da kashi 18.

Lalacewar aiyukan matatun na kunshe ne rahoton kudi na karshen wata da matatar ke badawa.

Rahoton na nuna cewa samuwar PMS wanda aka fi sani da fetur da kuma DPK wanda aka fi sani da kalanzir ya ragu ne daga lita miliyan 153.37 zuwa lita miliyan 125.86.

Kamar yanda matatar man fetur ta kasa ta fadi, raguwar samuwar su ya danganta ne da raguwar aikin Matatar man fetur ta Kaduna a wannan watan. Inda gyaran matatun da akeyi yanzu zai kawo cigaba matukar an kammala.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel