Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da zakaran zaben Osun, jam'iyyar APC ta yi nasara

Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da zakaran zaben Osun, jam'iyyar APC ta yi nasara

Labarin da ke shigo mana da dumi-dumi na nuna cewa hukumar gudanar da zab ta kasa mai zaman kanta ta alanta Alhaji Isiaka Gboyega Oyetola na jam'iyyar All Progressives Congress a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Shugaban zaben jihar Osun, ya sanar da cewa dan takaran jam'iyyar APC ya samu kuri'u 255,505 yayinda dan takaran jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 255,023

Tun misalin karfe takwas na safiyar yau Alhamis, 27 ga watan Satumba 2018, jami'an hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sun isa wurare bakwai da za'a karasa zaben jihar Osun.

Jami'an hukumar yan sanda da sauran jami'an tsaron sun mamaye wuraren domin tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ana gudanar da karashen zaben ne a wurare hudu:

1. Karamar hukumar Osogbo

2. Karamar hukumar Osogbo Ife ta arewa

3. Karamar hukumar Osogbo Ife ta kudu

4. Karamar hukumar Orolu

Ga jerin sakamakon kamar yadda suke a mazabun da aka gudanar da zaben

Orolu:

APC 280

PDP 122

Osogbo

APC 299

PDP 165

Ife ta kudu

APC 455

PDP 36

Ife

APC=126

PDP=2

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel