Bangar siyasa: Yan ta'adda sun kona motar wani dan takarar jam'iyyar APC a jihar Ondo

Bangar siyasa: Yan ta'adda sun kona motar wani dan takarar jam'iyyar APC a jihar Ondo

- Wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan ta'adda ne sun kai mummunan hari ga dan takara kujerar majalisa a Ondo, Olatayo Aribo

- Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan sun cinnawa daya daga cikin motpocin yakin zabensa wuta a yankin Owo da ke jihar

- Sai dai Aribo, ya ce tuni ya kai rahoton ta'addancin ga rundunar yan sanda

Dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya da zai wakilci mazabar Owo/Ose da ke jihar Ondo, Olayato Aribo, ya ga ta kansa bayan da wasu yan ta'adda suka kai masa mummunan farmaki wanda har suka samu nasarar kona motarsa.

Wakilin Legit.ng da ke a Ondo, Oluwaseun Akinbgoye, ya tattara rahoton cewa lamarin ya afku ne a Owo, shelkwatar karamar hukumar Owo da ke jihar, a ranar Laraba 26 ga watan Satumba, inda har yan ta'addan suka cinnawa motar dan takarar wuta.

KARANTA WANNAN: KARIN BAYANI: Yadda APC ta samu nasara a kananan hukumomi 3 cikin hudu na zaben jihar Osun

Bangar siyasa: Yan ta'adda sun kona motar wani dan takarar jam'iyyar APC a jihar Ondo

Bangar siyasa: Yan ta'adda sun kona motar wani dan takarar jam'iyyar APC a jihar Ondo
Source: Original

Majiya daga tushe ta bayyana cewa dan takarar, Aribo, baya cikin motar, sai dai mutane biyu daga cikin masoyansa ne da ke zagayawa da motar a yankin ofishin karba da aika sakwanni da wasiku da misalin karfe 10 na dare.

Bangar siyasa: Yan ta'adda sun kona motar wani dan takarar jam'iyyar APC a jihar Ondo

Bangar siyasa: Yan ta'adda sun kona motar wani dan takarar jam'iyyar APC a jihar Ondo
Source: Original

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ke cikin motar, Lanre Kako da kuma Tope, nankan hanyar su ta komawa gida inda suka tsaya sayen naman 'Suya', a dai dai lokacin ne yan ta'adsan suka far masu.

Wasu da lamarin ya faru akan idonsu, sun zayyana cewa yan ta'addan na zuwa suka budewa motar wuta da harbe harben bindigogi, suna mai cewa "wasu mutane ne suka zo muna zaune, kai tsaye suka ciro bindigogi suka fara harbin motar, daga bisani suka cinnawa kotar wuta, har sun tafi suka sakewa dawowa suka kara konata".

Sai dai da ya ke jawabi ga manema labarai a Akure, dan takar Aribo, ya ce baya zargin kowa da aikata masa wannan aika aikar, sannan tuni ya sanar da rundunar yannsanda don dakar mataki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel