Yadda aka kwashe yinin yau a ranar farko ta yajin aiki a Najeriya

Yadda aka kwashe yinin yau a ranar farko ta yajin aiki a Najeriya

- Yajin aikin kwana bakwai da kungiyar kwadago ta shirya, ya fara gurgunta aiyukan Gwamnatin tarayya

- An fara yajin aikin ne akan bukatar karin karancin albashi

- Karin albashin zai karfafa aiyukan tattalin arzikin kasar

Yadda aka kwashe yinin yau a ranar farko ta yajin aiki a Najeriya

Yadda aka kwashe yinin yau a ranar farko ta yajin aiki a Najeriya
Source: Original

Yajin aikin Jan kunne na kwanaki bakwai da kungiyar kwadago ta shirya, ya fara gurgunta aiyuka a sakateriyar Gwamnatin tarayya dake Abuja, a ranar Alhamis, wanda ita ce rana ta farko.

Ma'aikatan gwamnati a babban birnin tarayya sun kauracewa ofisoshin su wanda suke kulle a halin yanzu.

Majiyar mu da ta ziyarci harabar sakateriyar tarayya, ta lura da ofisoshin duk a kulle.

Ofishin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa, ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, kotun daukaka kara, ma'aikatu da cibiyoyi a birnin tarayya duk a garkame.

Ma'aikatar kudi da muhalli ma duk a kulle saboda yan kungiyar sunyi amfani da ababen hawan su gurin rufe hanyar shiga ma'aikatun.

Ofishin sakataren Gwamnatin tarayya ma ba kowa, sai dai akwai ma'aikata kadan da suka je aiki. Suma kuma hira sukeyi ba aiyuka ba.

DUBA WANNAN: Yadda ake kirga kwayar hatsi a kimiyyance

Yaran makaranta ma duk da sukaje makaranta, suna ta dawowa gidajen su saboda yajin aikin.

Duk da haka, yajin aikin bai shafi siye da siyarwa ba na wasu bangarori a birnin tarayyar irin su Kubwa, Mararraba, Karu, Gwagwalada da sauransu.

Kungiyar kwadagon ta shirya yajin aikin ne domin bukatar ta ta kara karancin albashi ga ma'aikatan kasar nan. A cewar su, hakan zai karfafa tumbatsar tattalin arzikin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel