Zaben Osun: ‘Yan sanda sun kama ‘yan PDP dake sojan gona a matsayin jami’an INEC, hoto

Zaben Osun: ‘Yan sanda sun kama ‘yan PDP dake sojan gona a matsayin jami’an INEC, hoto

Hukumar ‘yan sanda a jihar Osun ta bayyana cewar tayi nasarar kama wasu mutane dake sojan gona amtsayin jami’an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC ) a zaben raba gardama dake gudana yanzu haka a jihar Osun.

Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Osun, Folasade Odoro, ta bayyana hakan a wani jawabi da ta fitar ga manema labarai a yau, Alhamis.

Ta bayyana cewar an kama mutanen ne a karamar hukumar Orolu, daya daga cikin kananan hukumomin da ake maimaita zaben gwamnan jihar.

Zaben Osun: ‘Yan sanda sun kama ‘yan PDP dake sojan gona a matsayin jami’an INEC, hoto

‘yan PDP dake sojan gona a matsayin jami’an INEC
Source: Twitter

Kazalika ta bayyana cewar an samu wadanda kama din da katin shiadar zama mambobin jam’iyyar PDP amma kuma suna sanye da alamar dake nuna cewar su ma’aikatan INEC. Sannan ta kara da cewar suna amfani da kayan jami’an hukumar INEC domin shiga wuraren da bai kamata bad a kuma samun dammar taba kayan aikin zabe.

DUBA WANNAN: Zaben raba gardama a Osun: Sakamakon da suka shigo hannu

Bayan kayan hukumar INEC, an same su da Karin wasu kayan irin na masu saka ido lokacin gudanar da zabe.

Odoro ta kara da cewar babu gaskiya a cikin rahoton da ake yadawa cewar sun kama wasu masu aikin saka ido a zaben raba gardama na Osun tare da bawa mutanen jihar da masu ruwa da tsaki tabbacin cewar hukumar ‘yan sanda zata samar da isashshen tsaro domin ganin an kamala zaben lami lafiya.

Zaben Osun: ‘Yan sanda sun kama ‘yan PDP dake sojan gona a matsayin jami’an INEC, hoto

Kayan jami'an sa-ido da aka samu wurin su
Source: Depositphotos

Zaben Osun: ‘Yan sanda sun kama ‘yan PDP dake sojan gona a matsayin jami’an INEC, hoto

wata jaka irin ta masu aikin sa-ido da aka samu a wurinsu
Source: Depositphotos

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel