Raba gardama: Duba cikakken sakamakon zaben gwamnan Osun tsakanin APC da PDP

Raba gardama: Duba cikakken sakamakon zaben gwamnan Osun tsakanin APC da PDP

A yau, Alhamis, 27 ga watan Satumba, ne mutanen jihar Osun suka komawa filin zabe domin kada kuri’unsu a zaben raba gardama na gwamnan jihar da aka yi zagayen farko ranar Asabar.

Yanzu haka Gboyega Oyetola, dan takarar jam’iyyar APC ne a gaba a zaben bayan lashe mafi rinjayen kuri’u a kananan hukumomin Ife ta kudu, Ife ta arewa da Osogbo.

Ana gudanar da zaben raba gardamar ne a mazabu 7 dake kananan hukumomin jihar Osun 4 da suka hada da Ife ta kudu, Ife ta arewa, Orolu da Osogbo.

Ga jerin sakamakon kamar yadda suke a mazabun da aka gudanar da zaben

Orolu:

Mazaba ta 1:

APC 150

PDP 005

Mazaba ta 2:

APC 195

PDP 010

Mazaba ta 3:

APC 160

PDP 010

Orolu, mazaba ta 8, akwatu ta 4

APC 198

PDP 15

Orolu, mazaba ta 9, akwatu 3

PDP 64

APC 41

Karamar hukumar Ife ta kudu, akwatu ta 012

APC 283

PDP 15

Ife ta kudu

Mazaba ta 1.

APC 355

PDP 005

Mazaba ta 2.(Garage Olode)

APC 385

PDP 005

Mazaba ta 10, akwatu ta 02, karamar hukumar Ife ta arewa

APC 126

PDP 2

Ife ta arewa (Oyere)

APC 300

PDP 005

Mazaba ta 8, akwatu ta 10, karamar hukumar Ife ta kudu

APC 172

PDP 21

Mazaba ta 5, akwatu ta 17, karamar hukumar Osogbo

APC 299

PDP 165

Mazabar Oyęrę Aborisade dake Ife

APC=130

PDP=2

Mazabar Garage Olode Osogbo

APC-485

PDP-5

Mazaba ta 08, akwatu ta 001, a Kajola

APC 111

PDP 3

Yanzu haka APC ce a kan gaba da banbancin kuri’u fiye da 1,000 tsakaninta da jam’iyyar PDP.

Har yanzu hukumar INEC bata bayyana wanda ya lashe zaben ba, wannan sakamako ne da aka tattara daga mazabun da aka maimaita zaben na raba gardama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel