Yajin aiki: Kungiyar likitocin Najeriya ta yi hannun riga da kungiyar kwadago

Yajin aiki: Kungiyar likitocin Najeriya ta yi hannun riga da kungiyar kwadago

Kungiyar likitocin Najeriya reshen jahar Bauchi ta bayyana cewa basu tare da hadaddiyar kungiyar kwadago game da batun yajin aiki na dindindin da kungiyar ta kaddamar a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba, inji rahoton kamfanin dillancin labaru na Najeriya, NAN.

Shugaban kungiyar, Dr Lamara Dattijo ne ya sanar da haka a yayin wata hira da yayi da majiyar Legit.ng a garin Bauchi, inda yace kungiyarsu bata tare da kungiyar NLC; “Yayan kungiyarmu ba zasu shiga yajin aikin da kungiyar NLC ta kaddamar ba, saboda bama cikinsu.

KU KARANTA: Ma’aikata a jahar Kaduna sun yi fatali da batun shiga yajin aikin kungiyar kwadago

“Koda ma ba don haka, babu yadda za’ayi mu rufe asibitocin Najeriya gaba daya saboda wannan yajin aikin sakamakon akwai mutane marasa lafiya da dama a asibitocinmu, don haka kungiyarmu ta NMA tana sanar da jama’a cewa likitoci na nan a bakin aiki, bamu shiga yajin aiki ba.

“Muna kira ga hukumomin asibitoci dasu taimaka ma likitoci a yayin da suke gudanar da ayyukansu ta wajen tabbatar da tsaronsu da kuma basu damar amfani da kayayyakin aiki a asibitocin, haka zalika muna kira ga yayan kungiyarmu dasu cigaba da aiki tukuru ga marasa lafiya.” Inji shi.

Sai dai daga karshe Dakta Dattijo ya bukaci gwamnatin Najeriya da kungiyar kwadago dasu sasanta kansu don ganin yajin aikin ba dauki tsawon lokaci ana yins aba, domin yin hakan ne taimaki jama’an kasar gaba daya.

Da majiyarmu ta zazzagaya asibitocin jahar, ta samu likitoci da sauran ma’aikatan jinya na bakin aikinsu, musamman a babban asibitin koyarwa na jami’ar tunawa da Abubakar Tafawa Balewa, da kuma asibitin kwararru na garin Bauchi.

Sai dai a nasa bangaren, shugaban kungiyar ma’aikatan jinya na jahar Bauchi, JOHESU, ya tabbatar da goyon bayansu ga yajin aikin da kungiyar kwadago ta kaddamar, “Don haka mun tsunduma yajin aiki ba ji ba gani har sai mun samu sako daga shuwagabannin kwadago.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel