Gwamnatin Tarayya za ta yi nasara akan yakar cin hanci da rashawa - Buhari

Gwamnatin Tarayya za ta yi nasara akan yakar cin hanci da rashawa - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa, gwamnatin tarayya tana nan da daurin damarar ta kuma sanye cikin sulkenta na yaki domin ci gaba da fafatawa wajen tsarkake kasar nan da dukkan wani nau'i na cin hanci da rashawa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya a halin yanzu ta dukufa tare da sadaukar da kai domin cimma nasara kan yakar cin hanci da rashawa kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a birnin New York na kasar Amurka cikin jawabansa yayin halartar taron kungiyar kasashen Afirka ta AU (African Union) kan harkokin tsarkake nahiyyar daga babban kalubalen da take fuskanta na cin hanci da rashawa.

Kungiyar ta gudanar da wannan taro a wani bangare yayin taron majalisar dinkin duniya karo na 73 da ake ci gaba da gudanarwa a kasar Amurka dake nahiyyar Turai.

Gwamnatin Tarayya za ta yi nasara akan yakar cin hanci da rashawa - Buhari

Gwamnatin Tarayya za ta yi nasara akan yakar cin hanci da rashawa - Buhari
Source: Facebook

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, shugabannin kungiyar ta AU sun bai wa shugaba Buhari ragamar jagorancin al'amurra na yakar cin hanci da rashawa a nahiyyar baki daya.

KARANTA KUMA: Najeriya ta na bukatar jagora mai ilimi - Seriake Dickson

Shugaba Buhari ya yabawa shugabannin kungiyar dangane da wannan karamci na jagoranci da suka rataya a wuyansa tare nema goyan bayansu da kuma karfin gwiwa wajen yakar wannan mummunar annoba da ta yi kaka gida a nahiyyar.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, nahiyyar Afirka ta na asarar kimanin Dalar Amurka Biliyan 50 a kowace shekara ta hanyar cin hanci da rashawa kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana cikin jawabansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel