Ba a taba gurfanar da ni a Amurka ba - Wani Sanatan APC

Ba a taba gurfanar da ni a Amurka ba - Wani Sanatan APC

Sanata Ovie Omo-Agege mai wakiltan Delta ta Tsakiya ya ce babu wata kotu a kasar Amurka da ta taba samunsa da wani laifi.

Sanatan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke mayar da martani kan zargin da Jigo a jam'iyyar APC ta jihar Delta, Olorogun O'tega Emerhor ya yi na cewa wata kotun California ta bata samunsa da laifi.

Emerhor kuma ya yi ikirarin cewa Omo-Agege yana shirya mikircin yadda za'a halaka shi.

Ba a taba gurfnar da ni a Amurka ba - Wani Sanatan APC

Ba a taba gurfnar da ni a Amurka ba - Wani Sanatan APC
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yaki da rashawa: Magu ya yiwa 'barayin gwamnati' sabuwar albishir

Sai dai a wata sanarwa da Sanatan ya fitar a jiya Laraba ta bakin mai taimaka masa a fanin kafafen yada labarai, Efe Duku, ya ce wannan batun tsantsagwaron karya ce da sharri.

A jiya ne Emerhor ya shigar da kara ofishin sufeta janar na 'yan sandan Najeriya inda ya ce Sanata Ovie Omo-Agege yana shirin kashe shi kamar yadda sanarwan ta ce.

Sanarwan ta ce wannan ba komai ba ne illa sharri da neman bata sunan Sanata Ovie Omo-Agege kuma tuni Sanatan ya bayar da umurnin gudanar da bincike kan lamarin.

Duku ya ce an taba zargin Sanata Omo-Agege da aikata laifi a kasar jihar California da ke Amurka, amma daga karshe an wanke Sanatan saboda hakan duk wadanda su ke zarginsa da wannan laifin kawai suna neman ba ta masa suna ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel