Yanzu-yanzu: Yan ta'adda sun fara kwace katin zaben jama'a a Ifon

Yanzu-yanzu: Yan ta'adda sun fara kwace katin zaben jama'a a Ifon

Mazauna garin Ifon a karamar hukumar Orolu na jihar Osun sun kawo kukan yadda wasu yan barandan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun fara kwace musu katunan zabensu don hanasu kada kuri'a.

Game da cewar mazaunan, yan barandan sun dira unguwar rike da manyan makamai da ya kunshi bindigogi, adduna, kuma suna kwace katunan zaben mutane. Wannan abu ya hanasu iya kada kuri'arsu.

Daya daga cikin mazaunan da aka sakaye sunansa ya bayyanawa Sahara Reporters cewa: "Sun kwace mana katuna zabenmu; mun kasa kada kuri'a. Yan jam'iyyar APC ne."

Yanzu-yanzu: Yan ta'adda sun fara kwace katin zaben jama'a a Ifon

Yanzu-yanzu: Yan ta'adda sun fara kwace katin zaben jama'a a Ifon
Source: Facebook

A bangare guda, Hankalin jama'a ya tashi a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun yayinda aka fara harbe-harbe inda mutane suka fara neman mafaka.

A unguwar Idiya, Ward 8, Unit 1, kuma, karamar hukumar Orolu, wasu yan baranda sun fitittiki jama'a da suka fito kada kuri'a da safen nan. yanzu haka mutanen sun nemi mafaka a fadar Olufon of Ifon-orulu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel