Najeriya ta na bukatar jagora mai ilimi - Seriake Dickson

Najeriya ta na bukatar jagora mai ilimi - Seriake Dickson

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson, ya bayyana cewa kasar nan ta Najeriya tana da matsananciyar bukatar mai muhimmancin gaske wajen samun shugaban kasa mai cikakkiyar cancanta ta fuskar ilimi da zai fidda ita zuwa tudun tsira.

Lokaci ya karato da ya kamata kasar nan ta Najeriya ta samu jagora mai nagarta ta hangen nesa da zai ciyar da ita gaba tare da tabbatar da kwararar romo na dimokuradiyya kamar yadda Gwamna Dickson ya bayyana.

Cikin wata sanarwa da sanadin mai magana da yawun bakin gwamnan, Mista Fidelis Soriwei, ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin wani manemin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

Najeriya ta na bukatar jagora mai ilimi - Seriake Dickson

Najeriya ta na bukatar jagora mai ilimi - Seriake Dickson
Source: Depositphotos

Tambuwal ya ziyarci jihar fadar gwamna Dickson daka babban birnin Yenago a jihar ta Bayelsa tare da tawagarsa ta yakin neman zabe a yayin ci gaba da karade jihohin kasar nan domin samun wurin shiga da kuma goyon baya kan kudirin da ya sanya a gaba.

KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu tsofaffin 'Yan Majalisa 2 gaban Kuliya

Gwamna Dickson ya bayyana cewa, lokaci ya yi da ya kamata kasar nan ta samar da shugaban kasa mai tsarkakkiyar zuciya maras rauni na kabilanci da kuma nagarta ta rataya nauyin dukkanin al'ummarta a wuyansa ba tare da wani bambanci ba.

A cewarsa, ko shakka ba bu kuri'un al'ummar jiharsa ta Bayelsa na ga duk wani dan takara a zaben 2019 mai akida da kudiri na tunkarar sauya fasali da yiwa kasar nan garambawul.

A nasa jawaban, Gwamna Tambuwal ya nemi goyon bayan al'umma da kuma wakilai na jam'iyyar PDP reshen jihar, inda ya kuma jaddada kudiri da shan alwashin cika burikan kabilar Ijaw.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel