Yajin aiki: Kungiyar Kwadago ta rufe ofisoshi a filin tashin jirage na Murtala Mohammed a Legas

Yajin aiki: Kungiyar Kwadago ta rufe ofisoshi a filin tashin jirage na Murtala Mohammed a Legas

- Kungiyar Kwadago ta rufe ofisoshin kamfanonin sufurin jiragen sama da ke filin tashin jirage na Murtala Mohammed da ke Legas

- Kungiyar da dauki wannan matakin ne domin nuna rashin amincewar ga jan jiki da gwamnati ke yi wajen amincewa da sabon albashi mafi karanci

- Sai dai rufe ofisoshin bai hana fasinjoji da jiragen sama cigaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba ba

A yau, Alhamis ne Kungiyoyin Kwadago suka rufe ofisoshin kamfanonin jiragen sama da ke filin tashin jirage na Murtala Muhammed da ke Ikeja a Legas a yunkurinsu na tankwara gwamnatin tarayya ta amince da fara biyan sabon mafi karancin albashi.

Sai dai wannan matakin da suka dauka bai hana fasinjoji da kamfanonin jiragen sama cigaba da harkokinsu ba a wasu filayen tashin jiragen da ke kasar.

Kungiyar Kwadago ta rufe filin tashin jirage na Legas

Kungiyar Kwadago ta rufe filin tashin jirage na Legas
Source: Depositphotos

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa Kungiyar Kwadago na Kasa NLC, Kungiyar masu Sana'oi TUC da Hadadiyar Kungiyar Kwadago ULC duk sun bukaci mambobinsu su fara yajin aiki saboda rashin amincewa da karin albashin.

DUBA WANNAN: Kwartanci: An ajiye ma'aikacin gwamnatin jihar Katsina a gidan kaso

Kungiyoyin ma'aikata na sashin Sufurin jiragen sama kamar Air Transport Services Senior Staff Association of Nigeria (ATSSSAN), National Union of Air Transport Employees (NUATE) da Association of Nigerian Aviation Professionals (ANAP) duk sun rufe ofisoshinsu domin biyaya da umurnin kungiyar ta Kwadago na kasa.

Tun a jiya, mambobin kungiyar Kwadogon sun mamaye ofisoshin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama na kasa FAAN da Hukumar Kula da Sufurin Sama NAMA, sun koma rufe ofioshin Accident Investigation Bureau (AIB) and the Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA) at the Lagos airport.

A jawabin da ya yi, Mataimakin Sakatare Janar na ATSSSAN, ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa Kungiyar ba ta tsunduma cikin yakin aikin sosai ba saboda akwai jami'an su da suke tafi jihar Delta hallartan taro.

Ya shawarci gwamnatin tarayya da gagauta amincewa da amincewa da sabuwar albashin mafi karanci domin wannan kari ne da ya da ce ayi lokaci mai tsawo da ya wuce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel