Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu tsofaffin 'Yan Majalisa 2 gaban Kuliya

Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu tsofaffin 'Yan Majalisa 2 gaban Kuliya

Mun samu cewa hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta gurfanar da Sanata Sa'idu Kumo da kuma Honarabul Nuhu Puloma, a gaban babbar kotun tarayya dake jihar Gombe bisa zargin su da laifin almundahanar dukiya mai dumbin yawa.

An gurfanar da tsofaffin 'yan majalisar biyu gaban Alkali Nehizne Afolabi a ranar Larabar da ta gabata kamar yadda shafain jaridar The Punch ya ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin wannan jiga-jigai biyu da aikata laifi na almundahanar dukiya har ta kimanin N450m.

Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu tsofaffin 'Yan Majalisa 2 gaban Kuliya

Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu tsofaffin 'Yan Majalisa 2 gaban Kuliya

Jiga-jigan biyu sun yi tarayya da juna wajen kulla tuggun zambace wani ma'aikacin bankin Fidelity, Abba Sunday Agaba, inda suka karbe zunzurutun dukiya har ta N450m a ranar 27 ga watan Maris na 2015.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya da Jihohi sun gididdiba N741.84b a tsakanin su - FAAC

Legit.ng da sanadin shafin jaridar ta The Punch ta fahimci cewa, wannan tuggu ya sabawa sashe na 16 da na 18 cikin dokoki na bankunan kasar nan.

Sai dai kawowa yanzu Kotun ba ta tabbatar da wannan tuhuma ba inda ta bayar da beli kan N10m ga kowanensu tare da daga sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Dasumba domin ci gaba da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel