Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama mutane 4 dake hargitsa tsarin zabe a Osun

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama mutane 4 dake hargitsa tsarin zabe a Osun

- Jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun kama wani mutumi da ake ganin yana hargitsa tsarin zabe da ake sake gudanarwa a Osun

- An kama mutumin ne a mazaba ta 5, Ataoje E a Osogbo

- An kuma kama wasu mutane uku dauke da kayan tsafi

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun kama wani mutumi da ake ganin yana hargitsa tsarin zabe a wani mazaba a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

A cewar Channels TV an kama mutumin ne a mazaba ta 5, Ataoje E a Osogbo wacce ta yi rijistar masu zabe 884.

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wani mutumi da ya hargitsa tsarin zabe a Osun

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wani mutumi da ya hargitsa tsarin zabe a Osun
Source: Original

Haka zalika jami’an tsaro sun kama mutane uku da ake zargin suna dauke da kayan tsubbu da sauran abubuwan da aka haramta lokacin da ake gudanar da zaben jihar Osun.

An kama su ne a Osogbo inda ake gudanar da zaben.

Rahoto ya nuna cewa an kama wani mazaunin unguwar dake daukar hotuna daga harabar gidansa.

Duk wadannan na daga cikin yan kunne da akayi gabannin zaben.

A halin da ake ciki Legit.ng ta rahoto cewa a unguwuar Idiya, Ward 8, Unit 1, karamar hukumar Orolu, wasu yan baranda sun fitittiki jama'a da suka fito kada kuri'a da safen nan. yanzu haka mutanen sun nemi mafaka a fadar Olufon of Ifon-orulu.

Bayan wannan hari da aka kai Orolu, mazauna garin Disu sunce sun fasa kada kuri'a sakamakon cin mutuncin da akayi musu jiya. Sun bayyana cewa an hanasu fitowa daga gidajensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel