Yanzu Yanzu: Juyin mulki ne ke gudana a Osun ba zabe ba - Adeleke

Yanzu Yanzu: Juyin mulki ne ke gudana a Osun ba zabe ba - Adeleke

Dan takarar kujeran gwamna karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party a zaben jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya bayyana sake zaben dake gudana a mazabu bakwai na jihar a matsayin juyin mulki, jaridar Punch ta ruwaito.

Adeleke wanda yayi Magana da manema labarai akan wayar tarho ya bayyana cewa an hana magoya bayan PDP samun tyakardan dangwala kuri’a a zaben gwamna da ake sake gudanarwa.

Yanzu Yanzu: Juyin mulki ne ke gudana a Osun ba zabe ba - Adeleke

Yanzu Yanzu: Juyin mulki ne ke gudana a Osun ba zabe ba - Adeleke
Source: Depositphotos

"Abunda ke gudana a jihar Osun a yanzu ba zabe bane. Abunda muke gani juyin mulki ne. Abunda muke shaidawa kenan a yanzu.

“Ana tozarta magoya bayan mu sannan ba’a bari su jefa kuri’a ko kadan. Ya kamata duka duniya ta san cewa wannan ba damokradiyya bane,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jama’ar Lagas na tafiyar kafa tsawon mita da dama yayinda aka fara yajin aiki (hoto bidiyo)

A halin da ake ciki Legit.ng ta rahoto cewa a unguwuar Idiya, Ward 8, Unit 1, karamar hukumar Orolu, wasu yan baranda sun fitittiki jama'a da suka fito kada kuri'a da safen nan. yanzu haka mutanen sun nemi mafaka a fadar Olufon of Ifon-orulu.

Bayan wannan hari da aka kai Orolu, mazauna garin Disu sunce sun fasa kada kuri'a sakamakon cin mutuncin da akayi musu jiya. Sun bayyana cewa an hanasu fitowa daga gidajensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel