An gurfanar da wani mutumi a gaban kotu bisa zarginsa da sayar da zinaren bogi akan N500,000

An gurfanar da wani mutumi a gaban kotu bisa zarginsa da sayar da zinaren bogi akan N500,000

- An gurfanar da wani Abdullahi Abubakar, a gaban kotu akan zarginsa da sarwa wani mutumi sarkar zinare ta bogi akan kudi N500,000

- Sai dai wanda ake zargin ya ce bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba

- Babbar mai shari'a, Mrs Olufunke Sule Amzat, ta bada belin wanda ake zargin akan tarar N200,000

An gurfanar da wani Abdullahi Abubakar, mai shekaru 33 a gaban babbar kotun majistire dake Ikeja, jihar Legas a ranar Laraba, bisa zarginsa da ya sarwa wani mutumi sarkar zinare ta bogi akan kudi N500,000.

Abubakar, wanda ba a bayyana inda ya ke da zama ba, na fuskantar tuhua akan aikata laifuka guda biyu da suka hada da damfara da sata.

Dan sandan da ya shigar da karar, Benson Emuerhi, ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a cikin watan Yuli, a mashigar Aiye a yankin Isolo jihar Legas.

Emuerhi ya ce Abubakar ya karbi N500,000 daga hannun wani mutumi mai suna Mr. Abubakar Isah, wanda ya sayar masa da sarkar ta jabu.

An gurfanar da wani mutumi a gaban kotu bisa zarginsa da sayar da zinaren bogi akan N500,000

An gurfanar da wani mutumi a gaban kotu bisa zarginsa da sayar da zinaren bogi akan N500,000
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Anambra zata samu filin jirage na kasa da kasa idan har na zama shugaban kasa - Atiku

A cewar sa, an kari rahoton damfarar ga ofishin rundunar yan sanda, wadanda suka gayyaci wanda ake zargin don tuhumarsa. Sai dai wanda ake zargin ya ce bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.

Laifin da ake zargin Abdullahi da aikatawa ya ci karo da sashe na 287 da 323 na dokokin aikata munanan laifuka na jihar Legas, 2015. Sashe na 287 ya ce za a yankewa mai laifin hukuncin shekaru 3 a gidan kaso saboda aikata laifin sata, yayinda sashe na 323 ya ce a yankewa mai laifi shekaru 7 a gidan kaso saboda aikata laifin damfara.

Babbar mai shari'a, Mrs Olufunke Sule Amzat, ta bada belin wanda ake zargin akan tarar N200,000 tare da shaidu guda biyu da kotun za ta dogara da su, kana ta dage sauraron karar har sai 29 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel