Paris Club: An aikawa Gwamnatin Jihar Benuwai makudan kudi kuma an zare

Paris Club: An aikawa Gwamnatin Jihar Benuwai makudan kudi kuma an zare

- Kwanaki aka aikawa Jihar Benuwai makudan Biliyoyi domin biyan albashin Ma'ikata

-Yanzu dai Gwamnatin Tarayya ta zare kudin daga asusun Jihar ta bar jama'a da hamma

Paris Club: An aikawa Gwamnatin Jihar Benuwai makudan kudi kuma an zare

Gwamnatin Tarayya ta tura biliyoyi a asusun Jihar Benuwai ta kuma dauke
Source: Depositphotos

Mun ji labari cewa Ma’aikatar kudi ta bayyana cewa kwamitin FAAC da ke yin kaso na abin da Najeriya ta samu kowane wata ba ta bada gamsashiyyar amsa game da kudin da aka karbe daga Jihar Benuwai ba bayan an tura masu da aka yi.

Wani babban Jami’in Ma’aiktar kudi ya zanta da manema labarai jiya a babban Birnin Tarayya Abuja bayan taron da kwamitin tayi na karshen wannan wata inda yace bai san abin da ya sa aka zare kudin da aka aikawa wasu Jihohi daga baya ba.

An dai shirya cewa za a biya Ma’aikatan Jihar Benuwai kudin su ne kurum sai aka ji cewa an zare kudin daga asusun Gwamnatin Jihar. Hakan dai har ya kai wasu Ma’aikata sun yanke jiki sun mutu bayan su ji cewa babu su babu labarin kudin su.

KU KARANTA: Malaman da El-Rufai ya sallama daga aiki sun yi masa ruwan Al-kunut

Mahmoud Dutse ya bayyana cewa batun wannan kudi da aka turawa Jihohi bai shafi kwamitin FAAC ba domin ba aikin su bane. Dutse yace abin da ya kamata shi ne a nemi jawabi daga bangaren Gwamnati da ke da hannu a lamarin.

Sakataren din-din-din na Ma’aikatar kudin kasar Mahmoud Dutse ya ki sa baki a lamarin inda yace kwamitin na su ba ta zauna game da wannan batu ba. Dutse dai ya tabbatar da cewa Gwamnatin Kasar ta raba sama da Naira Biliyan 700 a watan nan.

Shugaban Kungiyar kwadago na Jihar Benuwai Godwin Anya yayi mamakin jin cewa Gwamnatin Tarayya ta karbe kudin da aka aikowa Jihar domin biyan Ma’aikata bashin albashin su na tsawon lokaci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel