An fara yajin aiki gadan-gadan a Najeriya

An fara yajin aiki gadan-gadan a Najeriya

- Kungiyoyin kwadago sun tsunduma cikin yajin aikin sai baba ya gani a fadin kasar

- Hakan ya biyo bayan rashin sasantawa tsakaninsu da gwamnatin tarayya

- Ya ce da alama gwamnatin kasar ba ta damu da halin da talakan kasar ke ciki ba

Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun tsunduma cikin yajin aikin sai baba ya gani a fadin kasar, saboda lamarin karin albashin ma'aikata.

A safiyar yau Alhamis, 27 ga watan Satiumba ne kungiyoyin suka fara yajin aikin a fadin kasar.

Hakan ya biyo bayan tashi baran-baran da aka yi a tattaunawar da suka kai daren jiya Laraba, 26 ga watan Satumba suna yi da gwamnatin Tarayyar akan lamarin sabon albashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar.

An fara yajin aiki gadan-gadan a Najeriya

An fara yajin aiki gadan-gadan a Najeriya
Source: Depositphotos

Kungiyoyin da suka hada da NLC da ULC da TUC sun dauki wannan mataki ne saboda abinda suka kira gazawar gwamnati wajen sauraron kokansu.

KU KARANTA KUMA: Direban Aso Villa ya yi yunkurin kashe kansa saboda karancin albashi

Kwamred Nasir Kabiru shi ne Sakataren tsare-tsaren hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa wato ULC a Najeriya, ya bayyana cewa masu daidaita da gwamnatin tarayya ba domin a cewarsa ana yaudararsu ne

Ya ce da alama gwamnatin kasar ba ta damu da halin da talakan kasar ke ciki ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel