Zaben 2019: Hukumar EFCC ta soma bibiyar kashe kudaden 'yan siyasa

Zaben 2019: Hukumar EFCC ta soma bibiyar kashe kudaden 'yan siyasa

- Hukumar EFCC ta soma bibiyar kashe kudaden 'yan siyasa

- Tace ta bullo da sabbin dubaru domin hakan

- Tace ta soma dabbaka hakan a zaben Osun

Hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta sha alwashin sake fitowa tare da anfani da dabarun zamani wajen bibiyar yadda 'yan siyasa suke kashe kudade a lokutan zaabe musamman ma wajen aikata ba dai-dai ba.

Zaben 2019: Hukumar EFCC ta soma bibiyar kashe kudaden 'yan siyasa

Zaben 2019: Hukumar EFCC ta soma bibiyar kashe kudaden 'yan siyasa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya zabi magaji

Hukumar haka zalika ta bayyana cewa ta soma dabbaka sabbin dubarun da ta bullo da su ne tun a zaben jihar Osun inda tace ta bibiyi sawun yan siyasa da yadda suke yawo da kudade wanda a cewar su ya taimaka wajen hana sayen kuri'u sosai.

A wani labarin kuma, Karamin ministan sufuri a bangaren zirga-zirgar jiragen sama na kasa Sanata Hadi Sirika a firar da yayi da manema labarai ya bayyana cewa kamfanin sufurin nan na jirgin sama mallakin Najeriya watau 'Nigerian Air' da yanzu haka aka dakatar bai taba rasa masu sa hannun jari ba.

Wannan dai na zaman tamkar martani ga ministan yada labarai na gwamnatin tarayyar, Alhaji Lai Mohammed da farko ya shaidawa 'yan Najeriya cewa rashin masu saka jari ne musabbabin dalilin dakatar da kaddamar da kamfanin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel