Girma ya fadi: Wani tsohon gwamna a Arewa ya shiga takarar dan majalisar wakilai

Girma ya fadi: Wani tsohon gwamna a Arewa ya shiga takarar dan majalisar wakilai

- Wani tsohon gwamna a Arewa ya shiga takarar dan majalisar wakilai

- Wasu na ganin bai dace ba

- Wasu kuma na ganin ai wannan na nuna rashin girman kai

Tsohon gwamnan jihar Kebbi dake a Arewa maso yammacin Najeriya watau Usman Dakingari mun samu labarin cewa ya sayi fom din takarar kujerar dan majalisar wakilai a jam'iyyar APC a zaben nan na 2019 mai zuwa.

Girma ya fadi: Wani tsohon gwamna a Arewa ya shiga takarar dan majalisar wakilai

Girma ya fadi: Wani tsohon gwamna a Arewa ya shiga takarar dan majalisar wakilai
Source: Twitter

KU KARANTA: Mahaifiyar Leah Sharibu ta kai Buhari kara

Wannan dai ya zo wa jama'a da dama a ba zata musamman ma ganin cewa shine ya zama gwamna na farko da ya fara yin hakan inda a baya gwamnoni kan zabi tafiya majalisar dattawa ne bayan kammala wa'adin mulkin su.

Legit.ng dai ta samu cewa gwamnan tuni har ya siya tare kuma da cika fom din takarar ta sa inda indan ya lashe zaben, yake sa ran wakiltar mazabar Suru da Bagudo a majalisar ta wakilai.

Sai dai yayin da wasu ke ganin hakan kamar ya kaskantar da kan sa ne, wasu magoya bayan sa kuma na ganin tsabar rashin girman kai ne irin na tsohon gwamnan kuma ma ya kamata a zabe shi saboda hakan.

A wani labarin kuma, Kimanin kwanaki uku kacal a shiga zaben fitar da gwani 'yan takarar gwamnonin jahohi a karkashin inuwar jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC, gwamnan Borno, Kashim Shettima ya zabi wanda yake so ya maye gurbin sa.

Wanda dai gwamnan ya bayyana goyon bayan sa a gare shi shine Farfesa Babagana Umara Zulum dake zaman kwamishinan gyara da kuma sake tsugunnar da wadanda ibtila'in ta'addancin Boko Haram ya shafa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel