Ko kadan ba na fargabar duk inda za a yi zaben fidda-gwanin PDP - Tambuwal

Ko kadan ba na fargabar duk inda za a yi zaben fidda-gwanin PDP - Tambuwal

Gwamnan Jihar Sokoto, kuma daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa ya yi na’am da duk wajen da za a gudanar da taron gangamin zaben fidda-gwanin jam’iyyar PDP na zaben shugaban kasa.

Tambuwal ya kasance daga cikin ‘yan takara 13 da ke neman tikitin PDP a matsayin wanda zai wakilci jam’iyyar a zaben shugaban kasa. Ya shiga takarar ne bayan ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Jam’iyyar PDP ta yanke cewa za a gudanar da gangamin a Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers. To sai dai kuma akwai wadanda suka nuna rashin amincewar su da haka.

Yayin da Kwamitin Gudanarwa na Kasa suka yarda a gudanar da taron a Port Harcourt, shi kuma Kwamitin Amintattun jam’iyyar ta nuna cewa har yanzu ba kai ga matsaya ba.

Ko kadan ba na fargabar duk inda za a yi zaben fidda-gwanin PDP - Tambuwal

Ko kadan ba na fargabar duk inda za a yi zaben fidda-gwanin PDP - Tambuwal
Source: Depositphotos

Adawar da wasu ke nunawa kan gudanar da taron a wani wuri ba Abuja ba ya samo asali ne saboda ganin da suke ana kunbiya-kunbiya ne don a baiwa Tambuwal tikitin.

Ana ta rade-radin cewa ana so a yi taron ne a wajen Abuja, domin a marawa Tambuwal bzyz, wanda ya kasanceaminin Wike ne, kuma wanda shi ne ke kashe wa jam’iyyar kudi, sannan kuma shakikin aminin Shugaban Jam’iyyar PDP ne, Uche Secondus.

KU KARANTA KUMA: Direban Aso Villa ya yi yunkurin kashe kansa saboda karancin albashi

Ana ganin daga Port Harcourt Wike zai iya taka rawa sosai wajen ganin Tambuwal ya yi nasara.

Sai dai kuma a lokacin da Tambuwal ke magana da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Niger ya ce bai damu ba, kuma ba ya fargabar duk garin da za a yi zaben fidd-gwani.

Tambuwal ya kuma kara da cewa ya na da yakinin idan har aka zabe shi a matsayin dan takarar PDP na zaben shugaban kasa a zaben 2019, to ya na da tabbacin zai iya kayar da Buhari.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Kebbi dake a Arewa maso yammacin Najeriya watau Usman Dakingari mun samu labarin cewa ya sayi fom din takarar kujerar dan majalisar wakilai a jam'iyyar APC a zaben nan na 2019 mai zuwa.

Wannan dai ya zo wa jama'a da dama a ba zata musamman ma ganin cewa shine ya zama gwamna na farko da ya fara yin hakan inda a baya gwamnoni kan zabi tafiya majalisar dattawa ne bayan kammala wa'adin mulkin su.

Legit.ng dai ta samu cewa gwamnan tuni har ya siya tare kuma da cika fom din takarar ta sa inda indan ya lashe zaben, yake sa ran wakiltar mazabar Suru da Bagudo a majalisar ta wakilai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel